Jakadan kasar Sin dake Nigeria Gu Xiaojie, da babban hafsan sojojin ruwa na yammacin tekun Nigeria Manjo Janar EG Ofik, da ma'aikatan ofishin jakadancin kasar Sin, da wakilan kamfanonin kasar, da Sinawa dake Najeriya kimanin 1000 ne suka tarbi jiragen ruwan.
Wannan rukuni dai ya fara wannan ziyara ne a kasashen Afrika 8, a daidai lokacin da ya kammala aikinsa na ba da kariya ga jiragen ruwa, dake sufurin makamai masu guba na kasar Sham a Gulf Ardan a ran 24 ga watan Afrilu.