Wadannan kudade za su shiga cikin ayyukan da za su taimaka wa wajen bunkasa noma da kuma karfafa muhimman gine ginen more rayuwar jama'a, ilimi da fasahohin zamani da sadarwa a nahiyar Afrika, in ji shugaban FEM, mista Philipp Rosler, kafin ya kara da cewa wadannan tsare tsare za su iya samar da moriya mai kyau a shekaru masu zuwa.
Wannan na nufin ba wai maganar kudi ba ce, har kuma damammaki ga nahiyar Afrika, kuma dalilin da ya sanya muka hadu nan, domin bullo da wadannan damammaki domin kyautata matsalar Afrika, in ji mista Rosler. Dandalin na kwanaki uku, kan taken "Yaya za'a gina wani tsarin bunkasuwa na musamman da samar da guraben aiki yi" ya kasance dandali na farko da aka yi a wata kasar dake yammacin Afrika.
A cewar mista Rosler, dandalin wannan shekara na daya daga cikin irin wadanda aka shirya cikin nasara a 'yan shekarun baya bayan nan.
Dandalin tattalin arzikin duniya na bana ya tattara mahalarta fiye da dubu daya wadanda suka yi magana da murya daya wajen murkushe matsalar ta'addanci da tashe tashen hankali a nahiyar Afrika. (Maman Ada)