Sanarwar ta bayyana cewa, kungiyar Boko Haram ta kai hare-hare a birnin Gamboru Ngala dake jihar Bornon Najeriya a ran 5 ga wata, lamarin ya haddasa mutuwa da jakkata mutane da dama. Kwamitin sulhu na MDD na kuma Allah wadai da hare-haren Boko Haram, a sa'i daya kuma, kwamitin ya nuna juyayinsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu cikin hare-haren kungiyar Boko Haram, da kuma jama'a da gwamnatin kasar, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.
Kwamitin sulhu na MDD ya ce zai ci gaba da mai da hankali kan halin da 'yan matan da aka sace suke ciki, da kuma batun daukar matakai kan kungiyar Boko Haram. Haka zalika, kwamitin ya jadadda cewa, duk wani ta'addanci ya kasance babbar barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, kuma babban laifin da ya kamata a hukunta. (Maryam)