in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnan Kano a tarayyar Najeriya ya yi Allah wadai da harin da aka kaddamar a jihar
2014-05-20 16:58:32 cri

Gwamnan jihar Kano dake arewacin Najeriya Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso, ya yi Allah wadai da harin bom da aka dasa a wata mota, a wani wuri dake kan titin Gold Coast a unguwar Sabon Garin jihar ta Kano da daren ranar Lahadin da ta gabata.

Gwamnan ya yi wannan bayani ne a yayin da kai ziyarar jaje ga mazauna unguwar a ranar Litinin.

Kwankwaso ya ce harin da aka kai unguwar ta Sabon Gari, hari ne da aka kaiwa Najeriya baki daya, saboda Sabon Gari unguwa ce dake da yawan kabilu daban-daban, daga sassa da dama na Najeriya. Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa, za ta yi iyakacin kokari wajen hada kai da sauran hukumomin tsaro, don kawo karshen irin wannan tashin hankali a jihar ta Kano.

Gwamna Rabi'u Kwankwaso ya kuma ce gwamnatinsa ta dauki nauyin jiyyar wadanda suka samu raunuka sakamakon wannan hari, wadanda a halin yanzu suke kwance a asibiti. Gwamnan ya kuma mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, tare da fatan samun sauki cikin sauri ga wadanda suka jikkata.

Da daren ranar Lahadi ne dai aka kai harin bom din na unguwar Sabon Gari dake jihar ta Kano, lamarin da ya hallaka mutane akalla 5, tare da jikkata wasu hudu. (Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China