in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gudanar da babban taron tattalin arzikin Afirka a Najeriya
2014-04-27 16:52:09 cri
Ya zuwa yanzu, shugabannin kasashe 10 da wakilai akalla 900 ne suka bayyana aniyar su ta halartar babban taron tattalin arzikin nahiyar Afirka da za a gudanar a birnin Abuja, fadar gwamnatin Najeriya.

A cewar kakakin tsara taron Ogbo Okiti, taron wanda ke tafe cikin watan Mayu mai zuwa, mai taken "daukar matakan samar da ci gaba, da samar da ayyukan yi" zai samu halartar wakilan gwamnatoci, da na manyan cibiyoyin kamfanonin kasa da kasa, daga kasashe 70, ciki hadda na nahiyar Afirka 30.

Okiti ya ce wannan ne karo na farko da za a gudanar da wannan taro a yammacin Afirka, lamarin da zai baiwa Najeriya dama daukacin yankin cikakkiyar damar cin gajiyar kyautata diplomasiyyar tattalin arziki, da ma harkar Al'adu. Kaza lika taron ya zo gabar da Najeriyar ta dare matsayin kasa mafi karfin tattalin arziki a Afrika, take kuma cika shekaru 100 da kafuwa a matsayin wata hadaddiyar kasa.

A wani ci gaban kuma, ministar kudin kasar Ngozi Okonjo-Iweala, ta mika wasikun tabbacin samun cikakken tsaro ga mahalarta taron dake tafe a ranar 15 ga watan nan. Har ila yau shima shugaban kasa Goodluck Jonathan ya jaddada hakan a ranar Alhamis. Yana mai bada tabbacin gudanar taron lami lafiya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China