in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 9 sun mutu a wani harin da aka kai a Najeriya
2014-05-02 16:20:43 cri
Hukumomi a Najeriya sun bayyana cewa,a kalla mutane 9 ne suka halaka kana aka garzaya da wasu 11 cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai zuwa asibitoci daban-daban da ke Abuja fadar gwamnatin kasar,sakamakon wani bam din da ya fashe ranar Alhamis da dare a wajen birnin na Abuja.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar(NEMA) da masu sanye da kayan sarki, sun bayyana cikin wata sanarwar hadin gwiwa cewa,sun kwashe gawawwakin mutane 9 a wurin da lamarin ya faru, yayin da mutane 11 da suka jikkata ke samun magani a asibitoci.

A wani sakon da ta aike wa 'yan Najeriya,hukumar ta NEMA ta tabbatar da cewa, fashewar ta auku ne a kusa da yadda aka kai harin bam din kunar bakin wake kwanakin baya a unguwar ta Nyanya,inda sama da mutane 75 suka mutu kana wasu 124 suka jikkata.

Ya zuwa yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai wannan hari.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China