in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda wasu ke yiwa ciwon hawan jini da na hakora rashin fahimta
2019-05-01 16:40:20 cri

Masu karatu, ko kun taba shan magani fiye da yadda likita ya kayyade domin shawo kan cututtuka? Ko kuna shan abubuwa masu gina jiki da sunan kiwon lafiya? Hakika dai, akwai rashin fahimta a wasu fannonin rigakafin cututtuka da kuma kiwon lafiya. Yau za mau gabatar muku bayanai ne wasu daga cikin wadannan fannoni.

Wasu suna ganin cewa, ciwon hawan jini, wani nau'in ciwo ne da ya fi kama tsoffafi, maimakon matasa. Amma hakika wasu nazarce-nazarcen da aka gudanar a ciki da wajen kasar Sin sun nuna cewa, kamuwa da ciwon hawan jini ba shi da wata alaka da shekarun mutum. Manyan dalilan da suke sa wasu su kamu da ciwon hawan jini su ne matsalar kiba, shan taba, shan giya da gado daga iyaye. Ban da haka kuma, gaggawa a rayuwa, da matsin lamba a wurin aiki da yanayin zamantakewar al'umma su ma suna da nasaba da kamuwa da ciwon hawan jini. Ana shawartar mutane da su ci abinci maras yaji, gishiri, man girki, da sukari, su kuma yi ayyukan da za su motsa jikinsu.

Masu karatu, kuna ganin, ciwon hakora, wani nau'in ciwo ne da tilas ne a je wajen likita? Wasu suna zaton cewa, idan hakoransu na ciwo, ba sai sun je wajen likita ba. Gaskiyar magana, idan baki babu lafiya, hakika baki dayan jiki ma babu lafiya. Cututtukan da ke shafar baki, kamar ciwon hakora, gyambon dasashi ko dasori da dai sauransu, suna iya lalata hakoran mutane da kuma sassan da ke kewayen hakoran baki daya, wadda daga karshe ya hana mutum tauna abinci, ko yin magana, har ya shafi kyan fuskar sa, ya kuma haifar da matsalar yin mu'amala da mutane da ma matsalar tunani. Kasancewar wasu kananan halittu masu rai cikin bakin mutane cikin dogon lokaci ya iya haddasa ko ma tsananta wasu cututtukan da suka shafi jikin mutanen baki daya, kamar ciwon zuciya da ciwon sukari da dai makamantansu.

Kwararru sun yi nuni da cewa, idan ana son yin rigakafin kamuwa da cututtukan da suka shafi baki, dole ne a rika goge hakora da safe da dare da kuma bayan cin abinci. Ya kamata duk mai iyali ya tanadi magogi ko bursohin goge hakori da kwaf dinsa, domin hana yaduwar cututtuka cikin iyali, kana a rika binciken lafiyar baki a kalla sau daya a ko wace shekara, kuma ya kamata rika zuwa asibiti ana wanke hakora sau daya a ko wace shekara. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China