in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka mutu a harin da aka kai a Najeriya ya karu zuwa 19
2014-05-02 20:24:56 cri
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana a ranar Jumma'a cewa,yawan wadanda suka mutu sakamakon harin bam din aka kai ranar Alhamis a wajen birnin Abuja ya karu zuwa 19.

Mai Magana da yawun 'yan sandan kasar, Frank Mba ya shaida wa manema labarai a wurin da lamarin ya faru cewa,mutane 60 da suka samu rauni na samun kulawa a asibitoci daban-daban da ke Abuja.

Ya ce ana nan ana gudanar da bincike game da musabbabin fashewar da rahotannin baya suka ce ta yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 9.

Wani wanda lamarin ya faru a kan idonsa ya ce wata mota ce kirar Volkswagen wadda aka ajiye ta a karshen hanyar Keffi ta tarwatse a kimanin nisan mitoci 50 daga inda aka kai harin ranar 14 ga watan Afrilu,lamarin da ya haddasa mutuwar sama da mutane 75 kana wasu 124 suka jikkata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China