in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nigeria ya canza niyyarsa ta ziyartar makarantar da aka sace dalibai mata
2014-05-16 20:43:16 cri
Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan a ranar jumma'an nan ya canza niyyar da yayi na ziyartar makarantar da aka sace 'yan mata fiye da 200 a garin Chibok na jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar wanda nan ne cibiyar kungiyar 'yan ta'addan nan na Boko Haram tun a shekara ta 2009.

Shugaban na Nigeria ya canza niyyar da yayi tun farko na ziyartar wannan makaranta ne safiyar jumma'an nan ne bisa wassu dalilai da ba'a bayyana ba,kamar yadda wani jami'in gwamnati ya sanar a Abuja babban birnin kasar.

Goodluck Jonathan yanzu zai tafi kasar Faransa halartar taron a kan tsaro wannan karshen makon bisa ga gayyatar da Shugaba Francois Hollande yayi masa wanda ya dauki nauyin shirya taron inji Rueben Abati kakakin Shugaban kasar.

Ana sa ran taron zai samu halartar shugabannin kasashen dake makwabtaka da Nigeria sannan zai maida hankali akan wannan kungiyar ta Boko Haram da kuma yadda za'a magance hare haren da take kaiwa al'umma.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China