in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimmancin musayar al'adu ga ci gaban bil-Adam
2019-05-16 09:05:53 cri

A ranar 15 ga watan Mayun shekarar 2019 ne, aka kaddamar da taron musayar al'adun nahiyar Asiya a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Taken taron shi ne, "Musayar ra'ayi da fasahohi tsakanin al'adu daban daban na nahiyar Asiya, gami da kafa wata al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. Ana sa ran a yayin taron, shugabannin kasashe daban daban da na kungiyoyin kasa da kasa za su tattauna yadda za a yi musayar al'adu gami da raba fasahohi tsakanin al'ummu daban daban.

An kuma gayyaci wakilai na kasashe 47 dake nahiyar Asiya, da suka hada da masana a fannonin adabi, da fasahohin al'adu, da Sinima, da tsoffin kayayyaki, da wadanda ke wakiltar malamai masu bada shawara ga gwamnati, da kafofin watsa labaru, da matasa, da sauran daidaikun mutane gami da wasu wakilan wasu kasashen dake wajen nahiyar Asiya

Taron ya kasance wani dandali mai kyau, inda za a iya musayar ra'ayoyi game da al'adu daban daban, da koyon fasahohin juna, don neman ci gaba tare.

Ana kuma saran taron zai kunshi bukukuwa fiye da 110, ciki har da baje kolin al'adu da abincin kasashen Asiya, da al'adun gargajiyar da aka gada daga kaka da kakani, da kuma fasahohin al'adu na Asiya, hakan zai baiwa jama'a cikakkiyar damar dandana al'adu daban daban da kansu da kara azama ga cudanyar al'adu tsakanin kasashen Asiya, da musayar ra'ayi tsakanin masu sana'ar yawon shakatawa na kasar Sin da na sauran kasashen nahiyar Asiya.

Masu fashin baki na fatan wannan taron, zai baiwa mutanen kasashe daban daban damar musayar al'adunsu masu kyau, da ci gaba da kokarin kafa wata al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakanin daukacin bil Adama. (Ahmed, Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China