in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani babban liman a Najeriya ya roki 'yan jaridu su daina danganta Boko Haram da kungiyar Musulunci
2014-05-19 20:48:06 cri

Babban limamin masallacin jami'ar Lead City dake Ibadan babban birnin jihar Oyo, Abdulrahman Muhammaed-Liawal, ya roki kafafen yada labaran Najeriya da su daina alakanta kungiyar nan ta Boko Haram da kungiyar Musulunci.

Babban limamin ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da kungiyar ma'aikatar gidan rediyon Najeriya, reshen birnin Ibadan suka gudanar, mai taken'Musulunci da kafar yada labarai'.

Malamin ya bayyana cewa ayyukan da kungiyar ta Boko Haram ke yi, sun saba wa koyarwar addinin Musulunci.

Ya ce "addinin musulunci,addini ne da ke koyar da zaman kafiya. Dabi'unsu ya saba wa na musulunci, dokar musulunci na nuna cewa duk wanda ya kashe wani hakkinsa yana kan wanda ya kashe shi. Don haka duk wanda ya san da wannan nauyi ba zai kashe wani ba".

Ya kuma roki kafafen yada labarai da su rika tantance labari kafin su yada shi, don kada su raba hankulan jama'a.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China