Faifan bidiyon ya nuna 'wassu 'yan matan na karatun Qurani sanye da hijabai a wani kebabben wuri da muryan wani namiji daga bayan su. Jim kadan da nuna bidiyon sai wadanda suka saka shi a yanar gizo suka cire da misalin karfe 12 da minti goma na rana agogon Nigeria.
Wani mutumin dake ikirarin shine Shugaban kungiyar Abubakar Shekau wanda tunda fari sojojin kasar suka ce sun kashe watannin 6 da suka gabata ya sanar da cewar ba za'a saki 'yan matan ba sai Gwamnati ta sako 'ya'yan kungiyar data kama,sannan yace daukacin daliban da suka sato sun musuluntar da su.
'Yan matan dai a yadda aka nuna su a bidiyon babu alamar cutuwa a gare su. A ranar litinin din data gabata ne kungiyar ta Boko Haram ta dauki alhakin satar 'yan matan a makarantar 'yan mata na garin Chibok dake jihar Borno a arewa maso gabashin Nigeria. (Fatimah Jibril)