in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
77 daga cikin 'yan matan da aka nuna cikin bidiyon Boko Haram an tantance fuskokin su
2014-05-14 20:48:11 cri
Daga cikin 'yan matan da kungiyar Boko Haram ta sace su sama da 200 a makarantar 'yan mata dake garin Chibok a jihar Barnon dake arewa maso gabashin Nigeria, wasu 77 da aka nuna a faifan bidiyon kungiyar data fitar jiya,an tabbatar da sunayen su.

Iyaye,Malaman makarantar dalibai da 'yan uwansu sun gane fuskokin wadanda aka nuna a faifan bidiyon lokacin da aka nuna shi a gidan gwamnati dake birnin Maiduguri,kamar yadda kakakin gwamnatin jihar Isa Gusau ya sanar.

A cikin wata sanarwar da ya sanya ma hannu Malam Isa Gusau ya yi bayanin cewa a cikin wadanda aka sabcen aka kuma nuna wassu a wannan faifan bidiyon,an tantance fuskokin 77 daga cikin su ta zayyana sunayen su da Iyaye, Malamai da masu gadin makarantar har ma da wassu daga cikin daliban da suka tsere bayan an sace su suka yi lokacin da suke kallon bidiyon. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China