in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 118 sun mutu a harin Jos na kasar Najeriya
2014-05-21 10:01:54 cri
Ma'aikatar tsaron lafiya ta Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa, fashewar bama-bamai a motocin bus ta auku har sau biyu a wata kasuwar da ke birnin Jos hedkwatar jihar Plateau a ranar Talata 20 ga wata, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 118 a halin yanzu.

'Yan sanda na kasar sun bayyana cewa, wadannan hare-hare biyu sun abku ne a kasuwar Terminus. Da farko an samu fashewar bam a cikin wani bus da ke kusa da cibiyar kasuwar, sannan jim kadan wani daban da ke da nisan mita 100 da bus din farko shi ma bam ya tashi a cikinsa. Yanzu an riga an kai wadanda suka raunuka asibiti don yi musu jinya.

Kawo yanzu dai babu wanda ya sanar da daukar alhaki kan harin. Amma 'yan sanda suna tuhumar kungiyar nan ta Boko Haram da wannan laifi.

A wannan rana kuma, shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya bayar da sanarwa, inda ya yi tofin Allah tsine da babbar murya kan lamarin. Yana mai cewa, wannan wani babban laifi ne na nuna rashin tausayi, don haka gwamnatinsa za ta yi iyakacin kokarinta wajen cimma nasarar yaki da 'yan ta'adda.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China