in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar tsaron Nigeriya sun kama wasu 'yan ta'adda a arewacin kasar
2014-04-24 20:54:35 cri
Rundunar tsaron sojin Najeriya ta tabbatar da kame wasu gungun 'yan ta'adda da suka yi sojan gona cewar makiyaya ne a jihar Taraba dake arewa maso gabashin kasar.

Kamar yadda Kakakin rundunar sojin kasar Manjo Janar Chris Olukolade yayi bayani a wata sanarwar da aka raba ma manema labarai, daya daga cikin 'yan ta'addan da aka kame ya tabbatar da cewar yana cikin 'yan ta'adda a jihar Borno da kwanan nan aka kai su zuwa garin Wukari a jihar Taraba domin ci gaba da ta da zaune tsaye a yankin.

Sanarwar ta ce an kashe wasu 'yan ta'addan a lokacin wani musayar wuta da sojoji a kan iyaka na kauyen gindin dorawa a wajen garin Wukari da ake binciken ababen hawa. Janar Olukolade ya kara da cewa an kuma samu manyan makamai na zamani da albarusai daga wajen 'yan ta'addan bayan da aka gano su sakamakon binciken da jirgin shawagi ya yi ta sama sannan aka bi maboyarsu, abin da ya yi sanadin musayar wuta.

Kakakin sojin ya ce za'a sassauta dokar hana fitan da aka saka a garin Wukarin da kewaye, amman jami'an soji za su ci gaba da zagaye tare da binciken gida gida. Wasu daga cikin wadanda aka kame sun tabbatar da cewa suke kai muggan kwayoyi ga 'yan kungiyar Boko Haram a wannan yankin. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China