140508murtala
|
Jami'an tsaron Najeriya dake gudanar da ayyukan bincike a yankunan arewa ta tsakiya, da yammacin kasar sun gano wasu makamai a wadannan yankuna.
A yayin wani binciken da suka gudanar a garin kira Anyibe dake karamar hukumar Logo ta jihar Benue, jami'an tsaron sun gano wasu makamai mallakar wani matashi, wanda ke cikin gungun masu tada zaune-tsaye a yankin. Jami'an tsaro sun gano bindigogi biyar, da wasu sauran makamai masu hadari. Yanzu haka dai ana tsare da wannan matashi domin ci gaba da bincike.
Haka kuma a jihar Plateau, jami'an tsaro sun gano bindigogi guda biyar da sauran wasu makamai, a wata mafakar 'yan ta da zaune-tsaye dake yankunan Hukke da Reweinko.
Labarai daga jihar Kaduna, wadda ke arewacin Najeriya ya shaida cewa, a yayin wani artabu da jami'an tsaro suka yi da 'yan ta da-kayar-baya a garin Kwandaga, mutane da dama sun samu raunuka, kuma an gano makamai da yawa.
Darektan yada labarai na hukumar tsaron kasar manjo-janar Chris Olukolade, wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja, ya ce binciken da ake gudanarwa a yankin yana daga cikin kokarin da hukumarsa ke yi, don ganin an samar da zaman lafiya a yankunan da ma kasa baki daya.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.