Wakilan matasan sun kuma yi wata zanga-zanga kan gazawar gwamnatin na daukar matakin ceto 'yan mata sama da 200 da aka sacen yau kusan sama da makonni uku.
Wannan lamari dai ya janyo hankulan jama'a a kasar Najeriya, inda ake ta yin kiraye-kiraye don neman taimakon kasashen waje, yayin da su ma iyayen yaran da sauran jama'ar Najeriya ke kira ga kungiyar ta Boko Haram da ta maido yaran ga iyalansu lami lafiya. (Ibrahim)