Rahotanni sun bayyana cewa Keshi ya fidda jerin sunayen ne a ranar Talata a birnin Abuja fadar mulkin Najeriya, bayan kammala zaman kwamitin tsare-tsare na hukumar kwallon kafar kasar. Ya ce 'yan wasan da aka zayyana za su bugawa kulaf din wasannin sada zumunci da kasashen Greece da Amurka da Scotland. Za kuma a sanar da sunayen 'yan wasa 23, da za a yi gasar cin kofin na duniya da su a ranar 2 ga watan Yunin dake tafe.
Yanzu haka dai ana sa ran 'yan wasan da aka gayyata za su isa sansanin kungiyar dake kasar Birtaniya, a ranar 25 ga watan nan na Mayu, domin shirin fuskantar takwarorin su na Scotland a wasan sada zumunci da tuni aka shirya bugawa ran 28 ga watan nan. Sai kuma wasannin sada zumuncin da Super Eagle din za ta yi da Greece ran 3 ga watan Yuni, yayin da wasan ta da Amurka zai kasance ran 7 ga watan na Yuni.
Sunayen 'yan wasan da aka fitar dai ya nuna cewa ba a gayyaci mai tsaron baya kungiyar Ike Uche ba, wanda aka maye gurbinsa da Leon Balogun, dake bugawa kulaf din Fortuna Dusseldorf na kasar Jamus kwallo. Shi ma a dan gaban kungiyar Bright Dike, wanda ya ci wa Super Eagles din kwallo a wasan sada zumunci da aka tashi 1 da 1 da Catalonia bai samu gayyatar ba.