in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cafke daya daga mutanen da ake zargi da kitsa harin Nyanya
2014-05-15 16:59:16 cri
Rahotanni daga tarayyar Najeriya na cewa an samu nasarar cafke Aminu Sadiq Ogwuche, daya daga mutane biyun da ake zargi da shirya kai harin Bam a unguwar Nyanya dake wajen birnin Abuja a tarayyar Najeriya. Harin da ya haddasa kisan mutane sama da 70, tare da jikkata wasu da dama.

Da yake karin haske game da hakan, shugaban hukumar wayar da kan jama'a ta tarayyar Najeriya NOA Mr. Mike Omeri, ya ce hukumar 'yan sanda ta duniya Interpol ce ta damke wanda ake zargin a kasar Sudan, za kuma a mika shi ga mahukuntan Najeriyar domin ya fuskanci hukunci.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China