in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarun kasashen waje basu shiga aikin ceton 'yan matan da aka sace ba
2014-05-11 20:16:36 cri
Rundunar sojin Najeriya ta karyata wasu rahotanni dake nuna yadda wasu dakarun kasashen ketare suka gudanar da sumame a cikin kasar.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar manjo Janar Chris Olukolade, ta ce kawo yanzu babu wani aikin soji da dakarun kasashen wajen suka yi, game da ceton 'yan matan da aka sace daga makarantar Chibok ta jihar Borno dake Arewa maso gabashin kasar.

Wannan dai sanarwa ta zo ne bayan da aka samu bullar wasu hotuna ta kafafen yanar gizo, dake nuna cewa wasu dakarun ketare sun gudanar da sumame a wani yanki na kasar, hotunan da a cewar Olukolade sam ma ba a Najeriya aka dauke su ba.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China