140513murtalakoubo.m4a
|
Obasanjo ya kuma yi kira ga wadanda suka sace daliban da su yi gaggawar sako 'yan matan domin ba su yi musu laifin komai ba, don haka kada su wahalar da su ba tare da hakkin komai ba.
"Kowane irin fushi wadannan mutane suke ji da shi, bai kamata a ce sun huce a kan yaran da ba su ji ba su gani ba." In ji Obasanjon.
"Don haka mun yi Allah wadai da abin da suka aikata, kuma muna kira gare su da su sako yaran, saboda suna da gudummuwa mai muhimmaci da za su iya bayarwa ga kasar a nan gaba", in ji tsohon shugaban kasar.
Har wa yau kuma, Obasanjo ya taya iyayen yaran jaje, amma kuma ya kara da cewa kada hakan ya sa wasu iyaye sun ki sanya 'ya'yansu mata makaranta. Ya kuma yi fatan za'a gano yaran, har a mika su ga iyayensu nan bada jimawa ba.(Murtala)