logo

HAUSA

 • In Ba Ku Ba Gida
 • Sin da Afirka
 • Duniya A Yau
 • Wasannin Motsa Jiki
 • Allah Daya Gari Bambam
 • Zhang Guimei: Taimakawa yara masu fama da talauci wajen samun ilmi yadda ya kamata

  Duk da cewa ba ta taba haihuwa ba, tana matukar kaunar dalibanta, kuma tana kaunar marayu, wadanda yara ne da iyayensu suka fito daga kananan kabilu masu fama da talauci a birnin Lijiang dake lardin Yunnan na kudu maso yammacin kasar Sin. Ta sadaukar da rayuwarta wajen taimakawa wadannan yara samun ilimi, haka kuma ta samarwa marayu matsuguni. Wacce mace ce mai kirki haka? Zhang Guimei ke nan, shugabar makarantar midil ta mata ta Huaping, kuma shugabar gidan marayu na Huaping.

  Duk da rashin isasshen lafiya, Zhang Guimei na aiki ba tare da gajiyawa ba wajen tabbatar da walwalar yaran. Cikin shekaru 20 da suka gabata, ta zama uwa ga marayu sama da 172, kuma tana matukar kula da su. Bisa tallafin gwamnatin karamar hukuma, da kuma mutane, Zhang ta taimakawa dubban ‘yan mata masu fama da talauci samun ilimi a makarantar Huaping cikin shekaru 12 da suka gabata. Sama da ‘yan mata 1600 daga makarantar, sun samu damar shiga jami’o’i. A watan Yulin 2020, ta samu lambar yabo ta mace mafi nagarta ta kasar Sin.

  Tun bayan sanar da sakamakon jarrabawar shiga jami’a a watan Yulin 2020, makarantar Huaping, wadda ita ce makaranta ta farko dake ba ‘yan mata ilimi kyauta a kasar Sin, wadda aka kafa a 2008, ta yi fice, inda kafafen yada labarai suka mayar da hankali kanta. Ko mene ne dalili? Saboda tana daga cikin makarantun Lijiang da dalibanta suka samu sakamako mai kyau yayin jarrabawar. Sai dai sakamakon bai gamsar da Zhang Guimei ba, ta ce tana sa ran dalibanta za su kara mayar da hankali kan karatunsu, ta yadda za su rage gibin dake akwai tsakaninsu da daliban sauran makaratun midil dake manyan birane. Zhang na cike da tunanin abubuwa masu dadi da marasa dadi da suka gudana cikin rayuwar aikinta.

  An haifi Zhang Guimei ne a Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang, kuma ta karanci harshen Sinanci a kwalejin ilimi ta Lijiang daga shekarar 1988 zuwa 1990. Jim kadan bayan kammala jami’a ne kuma ta auri Dong Yuhan, dan kabilar Bai. A shekarar 1990, ma’auratan suka koma garin Dong Yuhan, wato garin Xizhou, wanda ke kusa da gundumar Dali mai cin gashin kanta ta lardin Yunnan, domin aikin koyarwa a makarantar midil. Sai dai kuma, mummunar kaddara ta fadawa ma’auratan, inda sankarar ciki ta yi sanadin mutuwar Dong daga baya.

  Domin kauracewa abubuwan dake tuna mata da Dong, sai Zhang Guimei ta koma Huaping, wato wani yanki mai cike da tsaunika dake fama da talauci a watan Agustan 1996. Ta fara sabuwar rayuwa a makarantar midil ta Huaping Minzu, inda take koyar da Sinanci da harkokin siyasa ga manyan ajujuwa 4.

  A watan Afrilun 1997 kuma, Zhang ta gano tana da cutar kaba. Duk da cewa tana cikin ciwo, Zhang ba ta je asibiti ba har sai watan Yuli, bayan dalibanta sun shiga jarrabawar neman shiga babban sakandare.

  Bayan sun ji labarin rashin lafiyar Zhang, da yawa daga cikin mazauna Huaping, sun ba ta gudummuwar kudi da abinci. Saboda yadda ta ji dadin kulawar da suka nuna mata, Zhang ta yanke shawarar kara dagewa wajen kyautatawa mutanen.

  A watan Maris na 2001, bisa taimakon gwamnatin wurin, aka kafa gidan marayu na Huaping. An kuma ba Zhang Guimei shugabancin wannan gidan marayu. Kuma tun daga wancan lokaci, ta kaunaci marayun dake gidan. Cikin shekaru 20 da suka gabata, Zhang ta yi namijin kokari wajen kulla dangantaka mai karfi kamar ta jini a tsakaninta da marayun. Saboda yadda take kaunarsu, yara da dama na kiran Zhang da “mama”.

  Duk da taimakon kudi daga gwamnatin wurin, da kuma mutane masu tausayi suke bayarwa, Zhang Guimei tana matukar tattali wajen tafiyar da harkokin gidan. Duk da haka, ba ta taba yin kasa a gwiwa a kokarinta na taimakawa marayun ba. Haka kuma karin mutane sun yi ta ba gidan marayun gudummuwar kudi.

  A lokacin da take koyarwa a makarantar midil ta Huaping Minzu, Zhang ta kan bada gudummuwar kudi da kayayyakin amfanin yau da kullum ga yaran masu karamin karfi, domin taimaka musu yin karatu.

  Zhang ta kan damu da yanayin yaran, saboda galibinsu ‘yan mata ne da ba su samu ilimi mai kyau ba saboda iyayensu ba su da kudi kuma ba su yi karatu ba, don haka ba su gane muhimmanci ilimi ba.

  Domin taimakawa mutanen kauyen yaki da talauci da samun ci gaba, sai Zhang ta ga dacewar inganta matakin karatun ‘yan matan. “abun takaici ne yadda ‘yan matan suke fuskantar wariya wajen samun daidaito a fannin samun ilimi”, cewar Zhang.

  Zhang ta nemi taimako domin kafa babbar makarantar midil ta ‘yan mata. Sai dai, wasu mutane ba su fahimce ta ba, inda suka zarge ta da amfani da yara domin damfara.

  A watan Oktoban 2007, Zhang ta halarci babban taron JKS karo na 17 a matsayin wakiliya. Bayan taron, Zhang ta yi magana ta kafofi da dama ga jama’a game da burinta na kafa babbar makarantar midil ta ‘yan matan da suka fito daga gidajen matalauta a Huaping. Kuma cikin kankanin lokaci, Zhang ta samu tallafin kudi daga gwamnatin wurin da kungiyoyi daban-daban da mutane masu tausayi daga yankuna daban-daban na kasar Sin.

  Da taimakon gwamnatin wurin, Zhang ta kafa babbar makarantar midil ta ‘yan mata ta Huaping a watan Agustan 2008. A ranar farko ta zangon karatu na farko a makarantar wato ranar 1 ga watan Satumban 2008, dalibai 100 ne suka shiga makarantar. Galibin daliban sun fito ne daga iyalai matalauta na kananan kabilu a Lijiang. Kuma a kullum, Zhang kan busa algaita don tunatar da su lokacin shiga aji da na cin abinci da na motsa jiki, a kan kari. Galibin daliban na ganin Zhang na tsananta musu da yawa. 

  Ta hanyar bulaguro a hanya mai cike da tsaunika, cikin shekaru 10 da suka gabata, Zhang ta ziyarci sama da iyayen dalibai 1500 domin karfafa musu gwiwar tura ‘yayansu makaranta, ta yadda ‘yan matan za su iya inganta iliminsu da samun makoma mai kyau. A wani lokaci da ta hau babur domin ziyartar iyayen wata daliba, ta kasa kallon kasa saboda hanyar cike take da tudu da kwari. Ta yi fama da zazzabi, ta kuma some sau da dama yayin da take bulaguro domin ziyartar iyayen daliban.  

  Bisa la’akari da kokarin Zhang da sauran malaman makarantar, na taimakawa dalibai a fannin karatu, cikin shekaru 9 da suka gabata, dukkan daliban sun samu shiga jami’o’i da kwalejoji bayan sun lashe jarrabawar shiga jami’a ta kasa. A shekarar 2010, yawan daliban makarantar da suka shiga manyan jami’o’i ya kai kaso 4.26, yayin da jimillar ta karu zuwa kaso 44.02 a shekarar 2020, a don haka, makarantar ta kasance kan gaba cikin jerin makaratun midil mafi kyau a Lijiang, a fannin kyawun sakamakon jarrabawa. Yawancin daliban da suka kammala karatu, sun bayyana jin dadinsu na samun ilimi a makarantar, wadda ta ba su damar shiga manyan jami’o’in kasar Sin.  

  Da yawa daga cikin mutanen da suka san Zhang Guimei, sun yaba da jajircewarta kan aikinta, da kuma nacewa wajen taimakawa yaran masu karamin karfi samun ilimin domin sauya rayuwarsu.

  Duk da ba ta da isasshen lafiya, saboda fama da cututtuka 23 ciki har da sankarar kashi, Zhang na zama a cikin makarantar. Ayyuka sun mata yawa, ta kan tashi da karfe 5 na asuba, sannan ta kwanta da karfe 12 da rabi na dare.

  Yayin da take adana kudin da take samu da neman tallafi domin samar da yanayi mai kyau ga yaran kauyen, rayuwar Zhang ya mai da hankali ne kacokan kan aikinta. Duk da haka, ba ta taba yi wa wani korafi game da yanayin da take ciki ba. cikin shekaru 12 da suka gabata, Zhang ta taimakawa dubban ‘yan mata kasancewa a makaranta. Wannan kuma ya taimakawa makomar yaran. Yanzu haka sun girma kuma suna nasu ayyuka, galibinsu na taka muhimmiyar rawa a cikin al’umma.

  Zhang Guimei ta yi matukar jin dadi da yawancin tsoffin dalibanta suka bayyana sha’awarsu ta aiki a wurare masu nisa da koma baya, da nufin taimakawa mutanen yankin inganta rayuwarsu.

  Bisa la’akari da manyan nasarorin da ta samu, Zhang ta samu lambobin yabo da na girmamawa da dama, ciki har da lambar yabo ta ranar ma’aikata da ta mace mafi nagarta ta ranar 8 ga watan Maris. An kuma sanya sunanta cikin jerin malamai 10 mafi nagarta na kasar Sin.

  A watan Yulin 2020, Zhang Guimei ta kafa wata gidauniyar ilimi, domin amfani da gudunmuwar da ta samu daga kungiyoyi da mutane daban-daban wajen tallafawa ‘yan matan da iyayensu ba su da karfi a garin Lijiang.

  Yayin da labarin Zhang Guimei ya karade baki daya kasar Sin, jajircewarta ga samar da ilimi a Lijiang ya yi matukar burge mutane da dama. Zhang na farin ciki ganin ita da sauran malaman dake makarantar, sun zama tamkar tudun da yara ke iya hawa su hango kyawun da duniya ke da shi a wajen kauyensu.

  MORE
 • Balarabe Shehu Ilelah: Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta jagoranci kasar wajen samun dimbin nasarori

  Kwanan nan ne, Murtala Zhang ya samu damar zantawa da malam Balarabe Shehu Ilelah, babban darektan hukumar kula da harkokin yada labarai ta kafofin rediyo da talabijin ta Najeriya ko kuma NBC a takaice, wanda ya shafe shekaru da dama yana zaune a kasar Sin, inda ya bayyana ra’ayinsa kan muhimmiyar rawar da jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin ta taka, tun farkon kafuwarta har zuwa yanzu, wato lokacin da aka cika shekaru 100 da kafuwarta, musamman a fannonin da suka shafi kyautata rayuwar al’umma, raya tattalin arziki, yaki da cutar mashako ta COVID-19 da sauransu.

  Malam Balarabe ya kuma yi tsokaci kan sirrin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin a fannin jagorantar al’ummar kasar wajen samun dimbin nasarori.

  A karshe, malamin ya bayyana fatansa na ci gaba da inganta hulda da dankon zumunta tsakanin Sin da Najeriya da ma sauran kasashen Afirka. (Murtala Zhang)

  MORE
 • Yau take babbar sallah a sassan duniya

  A yau Talata 20 ga watan Yuli, daidai da ranar 10 ga watan Zhul Hajj bisa kalandar musulunci, miliyoyin al’ummar musulmin duniya ke gudanar da bukukuwan babbar sallah, wadda daya ce daga muhimman ranekun ibada na mabiya addinin Islama.

  Musulmi na gudanar da sallar Idin babbar sallah ne da hantsin wannan rana, kafin kuma su yanka dabbar layya, dake matsayin muhimmiyar ibada mai nasaba da ranar.

  Kafin ranar babbar sallah, a jiya Litinin, mahajjata dake kasar Saudiyya, sun gudanar da tsayuwar Arafa, wadda ita ce ibada mafi muhimmanci a ibadun aikin Hajji. Mahajjatan sun shafe sa'o'i da dama a filin Arfa, wanda shi ne filin da Manzon Allah (SWT) ya yi huɗubarsa ta ban kwana.

  Kamar bara, a bana ma kasar Saudiyya ta taƙaita yawan Musulman da suka gudanar da aikin hajjin zuwa mutum 60,000 kacal, kuma mafi yawan su mazauna kasar ne, a maimakon mutum kusan miliyan uku da kan yi aikin Hajjin a duk shekara. Saudiyya ta dauki wannan mataki ne da nufin tabbatar da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.

  A nan ma kasar Sin, dubun dubatar musulmi sun gudanar da sallah a masallatai daban daban, tare da aiwatar da matakan da suka wajaba na ba da kariya daga kamuwa da cutar COVID-19, duk da cewa a yanzu ba a samun yaduwar cutar a cikin kasar.

  Ana iya ganin musulmi sanye da kyawawan tufafi, suna gudanar da ibadu da hantsin wannan rana ta Talata, tare da sada zumunci, da yiwa juna fatan Alherin sake kewayowar wannan muhimmin biki.

  Bikin babbar sallah na alamta fatan musulmi na samun yardar ubangiji, da rahama da wadata. Lokaci ne kuma na murna, da ke cike da nishadi da annashuwa. (Saminu, Ahmad)

  MORE
 • Messi ya sadaukar da nasarar lashe kofin Copa America ga daukacin al’ummar Argentina da kuma Diego Maradona

  Tauraron kwallon kafar kasar Argentina da Barcelona FC Lionel Messi, ya ce ya sadaukar da nasarar da kungiyar kasar sa ta cimma, ta lashe kofin kwallon kafa na Copa America ga daukacin ‘yan kasarsa, yana mai fatan wannan nasara za ta taimaka wajen karfafa gwiwar al’ummar Argentina, a fannin yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

  Messi ya wallafa hakan ne kasa da kwana 1, bayan da Argentina ta lashe kofin na Copa America, a shafinsa na sada zumunta, yana mai cewa wasan karshen da suka buga da kasar Brazil ya kayatar. Ya ce “Mun san cewa muna da damar kara inganta kwarewar mu, amma a gaskiya ‘yan wasan mu sun yi namijin kokari wajen tabbatar da nasarar da muka samu, kuma hakan ya sa ni matukar alfahari, sakamakon sa’ar da na samu ta zama kyaftin din kungiyar mu a wannan karo”.

  Messi ya ce "Na sadaukar da wannan nasara ga iyali na, wadanda kullum ke karfafa min gwiwar kara azama, da abokai na da nake matukar kauna, da ma sauran mutane, da daukacin al’ummar Argentina miliyan 45 da suka jurewa wahalhalu, sakamakon fama da cutar COVID-19, musamman wadanda cutar ta shafi iyalin su.

  An dai buga wasan karshe na gasar kofin Copa America ne a filin wasa na Maracana dake Brazil, inda Argentina ta doke Brazil da ci 1 mai ban haushi, ta hannun dan wasan Argentina Angel Di Maria, matakin da ya kawo karshen shekaru 28 da kasar ta shafe tana jiran lashe wannan kofi.

  A cewar ma’aikatar lafiyar Argentina, ya zuwa yanzu sama da ‘yan kasar sama da su miliyan 4 sun harbu da cutar COVID-19, yayin da cutar ta hallaka sama da mutum 98,000.

  Don haka ne Messi, mai shekaru 34 da haihuwa, wanda aka baiwa kyautar tauraron gasar ta bana, ya ce ya sadaukar da kwallaye 4 da ya zura a raga, da tallafin zura karin wasu 5 da ya bayar yayin wannan gasa, ga tauraron kwallon kafar Argentina marigaji Diego Maradona, wanda ya rasu wasannin baya yana da shekaru 60.

  Ya ce "Wannan nasara ce ta daukacin ‘yan Argentina, da kuma Diego, wanda ko shakka babu ya taimaka mana daga inda yake” Messi ya kuma karfafawa ‘yan wasan kwallon kafar kasarsa gwiwar ci gaba da kwazon su, a fannin aiwatar da matakan dakile yaduwar wannan annoba.

  Ya ce "Domin ci gaba da shagulgula, dole mu kare kawunan mu. Kar mu manta muna da tafiya mai nisa kafin komai ya koma daidai. Ina fatan za mu yi amfani da damar mu ta wannan murna da muke yi, wajen karfafa ayyukan mu na yaki da wannan annoba tare."

  Kafin wannan, a ranar Lahadi, dan wasan Brazil Neymar, ya wallafa sako a shafin sa na yanar gizo, inda ya bayyana goyon bayansa ga sakon tsohon abokin wasan sa a Barcelona, kuma Aminin sa wato Messi.

  A sakon na sa, Neymar wanda a yanzu ke takawa PSG leda ya ce "Rashin nasara yana min ciwo. Abu ne da har yanzu ban saba da shi ba. A jiya, duk da mun yi rashin nasara, na je domin rungumar dan wasa mafi kwarewa da na taba haduwa da shi: Aboki na ne, kuma dan uwa na. Ina cikin damuwa, amma na fada masa cewa, "Jarumi, ka samu nasara a kan mu."

  "Ina cikin damuwar rashin nasara. Amma wannan gwarzo ne mai kwarewa! Ina matukar girmama irin gudummawar da ka bayar ga kwallon kafa, musamman gare ni. Bana son rashin nasara. Amma ina fatan za ka ji dadin wannan nasara, kwallon kafa ta jima tana jiranka."

  MORE
 • Ziyarar Faeza Mustapha a wasu sassan kasar Sin

  Kwanan baya, wakiliyarmu Faeza Mustapha ta samu damar ziyartar wasu sassa na kasar Sin. To, shin me ta gani a ziyarar? Yaya kuma ziyarar ta burge ta? A Kasance tare da mu cikin shirin Allah Daya Gari Bamban, don jin karin haske daga bakinta. 

  MORE