A yayin ganawar da suka yi da safiyar Talatar nan, Li Keqiang ya bayyana cewa, yana farin ciki da tattaunawar, bayan kammala ziyararsa a kasashen Afirka hudu da kuma kungiyar tarayyar kasashen Afirka.
Ya ce an kuma karfafa zumuncin dake tsakanin kasashen biyu a yayin ziyararsa a Najeriya, inda kasashen biyu suka samu sabon sakamako kan hadin gwiwarsu tare da zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare.
Haka zalika, a yayin ziyararsa a kasar, Mr. Li ya ganewa idanunsa bunkasar da kasar da samu, da kuma kyakkyawar makoman nahiyar Afirka baki daya.
Shi kuwa a nasa bangare, Mr. Mark ya taya wa firaministan kasar ta Sin murna bisa babbar nasarar da ya samu a yayin ziyararsa a kasashen Afirka. Ya ce, Najeriya ta yi maraba da godiya matuka ga ziyarar Mr. Li Keqiang a kasar, tare da halartarsa taron tattalin arziki na duniya kan Afirka da aka yi a birnin Abuja. Lamarin ya nuna zumucin dake tsakanin kasashen biyu, da kuma goyon baya ga gwamnati da jama'ar tarayyar Najeriyar.
Bugu da kari, Najeriya ta yi maraba da zuwan kamfanonin kasar Sin kasar, za ta kuma tabbatar da yanayin tsaron gudanar da ayyukansu a kasar, tare da ba su taimako yadda ya kamata. Kasarsa na fatan karfafa musaya da hadin gwiwar tsakaninta da kasar Sin, ta yadda za a iya ciyar da dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare gaba. (Maryam)