in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake samun fashewar wani abu a birnin Jos dake tsakiyar Najeriya
2014-05-25 15:30:05 cri
Rahotanni daga tarayyar Najeriya na cewa an sake samun aukuwar wani harin Bam a birnin Jos dake jihar Plateau, ko da yake dai kawo yanzu rundunar 'yan sanda, bata bayyana adadin mutanen da harin na daren Asabar ya ritsa da su ba.

Wannan dai hari ya auku ne 'yan kwanaki kadan da tashin wasu ababen fashewa biyu a birnin na Jos, wadanda suka haddasa rasuwar mutane sama da 118.

Da take karin haske game da lamarin, kakakin hukumar 'yan sandan jihar Felicia Anselm ta ce, an ta da Bam din ne a wani wuri dake kusa da jami'ar birnin Jos.

A hannu guda kuma wasu shaidun gani da ido sun ce an ga gawar mutumin da ake zaton shi ne yayi niyar kaddamar da harin kunar bakin waken, kusa wani gidan kallo yayin da ake tsaka da kallon wasan karshe na gasar cin kofin zakarun turai a daren na Asabar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China