Bisa labarin da kafofin watsa labarai na kasar Faransa suka bayar, an ce, shugaban kasar Francois Hollande ya bayyana a ranar 12 ga wata a Yerevan babban birnin kasar Armenia cewar, kasarsa ta riga ta gayyaci kasashen Amurka da Birtaniya wajen halartar taron da za ta shirya a birnin Paris bisa kokarin yaki da kungiyar Boko Haram mai tsattauran ra'ayin kishin Islama ta kasar Najeriya, wadda ta yi garkuwa da dalibai 'yan mata fiye da 200.
Shugaba Hollande ya kara da cewa, za a kira taron ne domin maida hankali kan wannan matsala, a maimakon jita jitar dake nuna cewa kasar Faransa za ta dauki matakin soja a kasar Najeriya. Haka kuma a yayin wannan taro za'a yi kokarin bullo da matakan yaki da kungiyar Boko Haram, kuma kasar Faransa za ta bada nata taimako.
Ya jaddada cewa, dole ne a yaki da kungiyar Boko Haram a maimakon neman sulhu tare da ita.(Kande Gao)