in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar kare hakkin mata ta yi kira da a sako 'yan matan da aka sace a wata jiha dake arewa maso gabashin Nigeria
2014-04-24 15:32:29 cri
Kungiyar kare hakkin mata dake jihar Borno, wace ke arewa maso gabashin Nigeriya, sun kara yin kira akan kungiyar Boko Haram da su sako sauran 'yan mata 230 da suka sace daga wata makaranta.

Matan da ke kungiyar kare hakkin mata ta Baobab, sun bukaci kungiyar ta Boko Haram ta sallamo 'yan matan dake makarantar sakandaren gwamnatin 'yan mata ta Chibok ba tare da gindaya wani shinge ba.

Kakakin Kungiyar Hauwa Biu, ta shaidawa wani taron manema labarai a Maiduguri, fadar gwamnatin jihar Borno cewar, sace 'yan matan da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi wani abu ne da ya sabawa yancin 'yan matan.

Hauwa Biu ta jaddada cewar, yin awon gaba da 'an matan, aikata laifi ne ga bil adama, kuma kamar yadda tace matan jihar Borno suna kira da babbar murya akan 'yan Boko Haram da su sako illahirin 'yan matan dake hannnun su, ba tare da sun cutar da su ba.

Biu, ta yi kira akan jami'an tsaro da su yi amfani da makamai na zamani domin gano takamaiman wurin da masu sace 'yan matan suke zaune, domin gudanar da aikin ceto ba tare da wata matsala ba. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China