140518Bagwai.m4a
|
A ranar Asabar 17 ga wata hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano ta gudanar da zaben kananan hukumomi a daukacin kananan hukumomin jihar 44, to sai dai kuma zabe ya zo da wasu matsaloli da suka hadar da rashin zuwan kayan aiki a kan lokaci da kuma rikici tsakanin magoya bayan jam`iyyu.
Shi dai wannan zabe wanda aka jima ana dakonsa ya zo daidai lokacin da hada hadar babban zaben kasa na 2015 ke kunno kai, a inda jam`iyyar PDP mai jan ragamar kasar ke gwagwarmayar kwatar kai daga barazanar jam`iyyar hadaka ta APC ko da yake akwai wasu jam`iyyun na daban da su ma suke hasashen yin tasiri a zabukan.
A jihar Kano zaben da aka gudanar na kananan hukumomi a ranar Asabar din nan zai iya kasancewa mizani na auna karfin jam`iyyun biyu a manyan zabuka masu zuwa.
Hakika jinkirin gudanar da zaben kananan hukumomi a Kano, da gwamna Dr. Rabi`u Musa Kwankwaso ya yi, masana harkokin siyasa na ganin ya shafi kwarjinin jam`iyyar ta APC musamman a tsakanin `yan jam`iyya wadanda aka taho da su tun lokacin da gwamnan yake cikin jam`iyyar PDP .
Ko da yake wannan ba za ta hana jam`iyyar taka rawa ba a wannan zabe da aka gudanar, amma irin cikas din da aka ci karo da su a zaben, musamamn rashin isowar kayan aiki a wasu mazabu kan lokaci da karancin jami`an tsaro a wasu mazabu da kuma rikici da aka fuskanta a tsakanin magoya bayan jam`iyyun PDP da APC ya yi matukar rage armashin zaben.
A bisa ka`ida za`a fara gudanar da zabe tun da karfe takwas na safe a kowace mazaba, amma a wasu yankuna sai karfe uku na rana aka fara wasu kuma karfe goma yayin da wasu mazabun aka fara kada kuri`a karfe tara .
Ko da yake rahotanni sun tabbatar mun cewa a karamar hukumar Kunchi dake arewacin jihar Kano, an kammala zabe tun karfe 11 na safe, ba tare da talakawa sun kada kuri`arsu ba, wannan ce ta sanya ma jam`iyyar adawa ke zargi an tafka magudi a zaben.
A can mazabar Kafin mai yaki kuwa dake yankin karamar hukumar Kiru, rahotanni sun bayyana cewa a kalla mutane uku ne suka rasa rayukansu, lokacin da `yan sanda suka yi ta harbi sama bayan da wasu 'yan siyasa suka yi kokarin kwashe kayayyakin zabe dake wata motar hukumar zabe.
A mazabar Shuwaki dake yankin karamar hukumar Tudun Wada rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutane biyu yayin wata hatsaniya ta barke tsakanin magoya bayan jam`iyyar APC da PDP.
Duk wani kokarin da na yi domin jin ta bakin kakakin rundunar `yan sandan jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya a kan wadannan rikice rikice abun ya ci tura.
Daya wa daga cikin mazabu dai ba su samu isassun jami`an tsaro ba duk da cewa babban sifeton `yan sanda Najeriya ya bayar da izinin tura karin `yan sanda jihar Kano domin su taimaka wajen gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.
Ana sa ran samun cikakken sakamakon zabukan a ranar Lahadin nan, daga bakin shugaban hukumar zaben ta jihar Kano Alhaji Sani Lawal Malunfashi, duk da cewa dai dokar ta bayar da damar a rinka sanar da sakamakon kowacce mazaba da zarar an kammala kada kuri`a musamman zaben kansuloli. (Garba Abdullahi Bagwai)