Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwararsa na kasar Afrika ta kudu Maite Nkoana-Mashabane a yau Laraba 14 ga wata a birnin Pretoria na Afrika ta kudu.
Yayin ganawar tasu, Mr Wang ya ce, bisa bukata da tsarin raya Afrika ta kudu, ya ba da shawarar kara yin hadin gwiwa tsakaninsu a fannoni shida, wato hadewar masana'antu da karfin samar da kayayyaki, har ma da bunkasa yankin musamman na tattalin arziki, da ayyukan dake kan teku, da kuma manyan ababen more rayuwa, albarkatun kwadago da hada-hadar kudi. A sa'i daya kuma, ya kamata bangarorin biyu su kara yin cudanya tsakanin manyan shugabannin kasashen biyu da yin mu'ammala ta fuskar al'adu da kara tattaunawa tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a samar da tsari mai kyau da samun goyon bayan jama'a wajen tabbatar da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
A nata bangare kuma, Maite Nkoana-Mashabane ta nuna cewa, Sin da Afrika ta kudu suna nuna ma juna goyon baya, da amincewa da juna da kawo moriyar juna. Kuma kasarta na mai da Sin sahihiyar kawarta a duniya kuma muhimmiyar abokiyarta wajen tabbatar da tsarin raya Afrika ta Kudu.
Dadin dadawa, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayi kan dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika karo na shida da za a shirya, idan suka cimma matsaya daya wajen gudanar da shi cikin hadin gwiwa.(Amina)