in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shiga wani sabon zamani a kokarin karfafa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka
2014-03-08 12:12:28 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce an shiga wani sabon zamani a kokarin karfafa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka.

Ministan ya bayyana haka ne a yau Asabar 8 ga wata lokacin da yake zantawa da manema labarai a wani gefe na cigaban babban taron majalissar wakilan jama'ar kasar da yanzu haka yake gudana.

Yayin da yake amsa tambayar wakilin gidan telabijin din kasar Afirka ta Kudu, ya yi bayani kan huldar dake tsakanin Sin da nahiyar Afirka, inda ya ce, za a iya takaita huldar dake tsakanin bangarorin 2 da jimloli 3:

Wato da farko, kasar Sin da kasashen Afrika 'yan uwa ne da suka taso tare ,ya ce, kafin kasar Sin ta fito daga kangin talauci, ta yi kokarin tsimin kudi don tallafawa fafutukar kasashen Afirka ta fuskar neman 'yancin kai, yayin da kasashen Afirka a lokacin suka taimaka sosai wajen maido da kujerar Sin cikin MDD.

Ban da wannan, a cewar minista Wang Yi, kasashen Afirka da kasar Sin kawaye ne dake kokarin hadin gwiwa da juna cikin daidaituwa. Sannan kuma yayin da take hulda da kasashen Afirka, Sin ba ta taba nuna girman kai ba, balle ta tsoma baki cikin harkokin gidan kasashen su. Sa'an nan duk wani alkawarin da Sin ta yi, tana cikawa.

Wang a cigaba da bayaninsa ya bada misalin cewa, ya zuwa yanzu Sin ta na cigaba da taimakawa kasashen Afirka wajen gina wasu manyan ayyukan da yawansu ya wuce 1000, inda ba ta taba sanya sharadi a ciki ba. A cewarsa, wannan bayanin kadai zai iya wanke kasar Sin daga zargin da ake yi mata.

A bayanin sa na uku, minista Wang Yi ya ce game da yanayin huldar Sin da Afirka, za'a iya cewa bangarori ne 2 dake kokarin samun ci gaba tare. Ya ce, a lokacin da ya ziyarci nahiyar Afirka a watan Janairun bana, abokanansa na kasashen Afirka da yawa sun gaya masa cewa, daya daga cikin dalilan da suka sanya nahiyar Afirka ta samu ci gaba sosai a shekarun baya a fannin tattalin arziki shi ne domin hadin gwiwar da kasar Sin take yi da su abin da ya sa kaimi ga sauran kasashen da su kara zuba jari ga nahiyar Afirka.

A karshen maganarsa, ministan ya ce, shekarar bana ita ce zagayowar shekarar ta 50 bayan da tsohon firaministan kasar Sin Zhou Enlai ya fara kokarin kulla hulda da kasashen Afirka. Sa'an nan abokantakar dake tsakanin Sin da Afirka zai dore, ganin yadda shugaba Xi Jinping ya kai ziyara ga wasu kasashen Afirka a bara, kana firaministan kasar na yanzu Li Keqiang shi ma zai ziyarci nahiyar Afirka a cikin wannan shekarar, wanda zai kasance karon farko da mista Li ya ziyarci nahiyar bisa matsayinsa na firaministan kasar Sin. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China