A kasar Kenya, mista Wang ya shawarta cewa kasashen biyu suna hada dangantakarsu a cikin muhimman bangarori bakwai, kamar zamanintar da aikin noma, bunkasa ababen more rayuwa, makamashi mai tsabta, domin kara zurafa hulda da abokantaka tsakanin kasashen biyu.
A kasar Kamaru, mista Wang ya bayyana cewa kasar Sin zata cigaba da kyautata yardar juna ta fuskar siyasa tare da kasar Kamaru, bunkasa dangantakar moriyar juna, bisa tushen bukatun cigaba na kasar Kamaru da kuma kwarewar Sin.
A kasar Guinee Equatoriale, ministan harkokin wajen Sin ya sanar da cewa kasar Sin zata cigaba bunkasa dangantaka tare da kasar Guinee a bangaren makamashi da ma wasu bangarori.
A kasar RDC-Congo, babban jami'in diplomasiyyar kasar Sin ya bayyana cewa ya kamata Beijing da Kinshasa su cigaba da tallafawa juna ta fuskar siyasa, neman sakamako na moriyar juna a fannin tattalin arziki, da kuma zurfafa dangantaka a bangaren tsaro.
Bayan karfafa huldar siyasa da dangantakar tattalin arziki, wani muhummin bangare na ziyarar mista Wang a nahiyar Afrika shi ne na kawo goyon bayan kasar Sin ga hukumar cigaban kasa da kasa ta IGAD, wato kungiyar shiyyar dake kunshe da kasashen gabashin Afrika guda takwas, domin maido da zaman lafiya da zaman karko a Sudan ta Kudu.
Har wa yau a yayin wannan rangadi nasa, ministan harkokin wajen kasar Sin ya gana da manyan jami'an IGAD da kuma bangarorin dake gaba da juna a kasar Sudan ta Kudu a ranar 12 ga watan Janairun a Khartoum babban birnin kasar Sudan.
A yayin wannan ganawa, bangarorin dake yaki da juna a Sudan ta Kudu sun samu amincewa da juna domin gaggauta shirin wanzar da zaman lafiya a cikin kasar tare da kuma nuna godiyarsu ga kasar Sin kan taimakonta game da kokarin shiga tsakani na kungiyar IGAD. (Maman Ada)