A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya shugabanci taro karo na 9 na kungiyar kula da ayyukan kudi da tattalin arziki karkashin shugabancin kwamitin tsakiya na JKS., inda aka saurari yadda aka aiwatar da muhimman ayyukan da kungiyar ta tsara, alal misali, shirin raya birane na zamani, tabbatar da samun isashen abinci, ruwa da makamashi, kafa bankin zuba jari kan ayyukan more rayuwar jama'a na Asiya, kafa asusun hanyar siliki da dai sauransu, har wa yau kuma an dudduba da yin nazari kan kundin shirin raya biranen Beijing, Tianjin da lardin Hebei tare.
A yayin taron, shugaba Xi ya jaddada cewa, wajibi ne a aiwatar da ayyukan kungiyar kula da ayyukan kudi da tattalin arziki karkashin shugabancin kwamitin tsakiya na JKS. yadda ya kamata, tare da yin hadin gwiwa da sassa daban daban. Har wa yau tilas ne a mai da hankali wajen an samu sakamako da ya dace, a tafiyar da ayyukan daidai lokacin da aka tsara yadda ya dace, a kokarin tabbatar da samun sakamako wajen aiwatar da manufofin JKS yadda ya kamata. (Tasallah)