Jiya Jumma'a 28 ga watan Febrairu, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi wani muhimmin jawabi a nan Beijing, inda ya ce, idan jama'ar kasar suna da imani, to, al'ummar kasa za ta iya samun makoma mai haske, kuma kasar za ta samu karfi. Yayin da ake kokarin cimma burin farfado da al'ummar Sin, ba akwai ana bukatar dimbin dukiyoyi ba, har ma ana bukatar rika kyautata da'ar jama'a.
Shugaba Xi ya fadi haka ne a yayin da yake ganawa da wakilan nagartattun ma'aikatan kula da kyautata da'ar jama'a a birane da yankunan karkara da hukumomi da kuma kyautata da'ar yara manyan gobe a wannan rana a Beijing.
Shugaban kasar Sin ya nuna cewa, yanzu haka ya zama dole mu yi amfani da lokacin da ake da shi kamar yadda ya dace, mu yi amfani da sabbin hanyoyi da kuma rika kyautata hanyoyin da aka saba bi a baya wajen kyautata da'ar al'umma. Kamata ya yi mu mayar da bukatun jama'a a gaba da kome, mu dauki hakikanin matakai domin samun sakamako na a-zo-a-gani, yayin da muke kyautata da'arsu. Za mu yi iyakacin kokarinmu wajen biyan bukatun jama'ar kasar na kyautata da'arsu. (Tasallah)