Cikin sharhin da People's Daily ta fitar a yau Lahadi, an ce, cikin tunanin fannoni hudu da shugaba Xi Jinping ya sanar, gudanar da ayyukan jami'yyar kwaminis ta Sin yadda ya kamata na nuna aniyar hada harkokin jam'iyyar da harkokin kasa tare, ya kamata a gudanar da harkokin jam'iyyar bisa babban tsarinmu yadda ya kamata, yayin da ake ci gaba da nuna manufofin jam'iyyar bisa fannoni daban daban, lamarin ya biya bukatun jam'iyyar kwaminis ta Sin da jama'ar kasar baki daya.
Kaza lika, sharhin ya nuna cewa, jagoranci na jam'iyyar kawaminis shi ne tushen tunanin fannoni hudu, babban alhakin 'yan jam'iyyar kwaminis shi ne na tsayawa tsayin daka wajen gudanar da harkokin jam'iyyar yadda ya kamata da kuma daga dukkan fannoni, ta yadda jam'iyyar za ta iya kasancewa babban karfi na ba da jagoranci, tare da tabbatar da cimma burinmu na farfadowar kasa ta Sin. (Maryam)