in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya jaddada muhimmancin aiwatar da manyan kudurorin gyare-gyare
2015-04-01 19:59:13 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga dukkanin sassan masu ruwa da tsaki game da aiwatar da gyare-gyare, da su kara azama wajen ganin an cimma nasarar burin da aka sanya gaba, game da kudurorin nan na kawo sauyi guda 4.

Shugaba Xi, wanda ya bayyana hakan yayin da yake tsokaci a taro na 11, na manyan jami'an dake aikin zurfafa gyare-gyare, ya kara da cewa ya zama wajibi ga daukkanin wadanda wannan nauyin ke kansu, su zage damtse, tare da nuna jarumta, domin kaiwa ga cimma nasarar da aka sanya gaba.

Ya ce akwai bukatar kara azama a fannonin jagoranci, da na tsare-tsare, da yayata manufar sauye-sauyen, da kuma aiwatar da su. Shugaban na Sin ya kuma kara da cewa dole ne sauye-sauyen da ake aiwatarwa su zamo daidai da bukatun al'ummar Sinawa. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China