in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin waje na kasar Sin ya gana da takwarorinsa na Amurka da Rasha
2014-11-24 21:01:34 cri
Ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov a lokacin shawarwari kan batun nukiliyar kasar Iran. Yayin ganawar, Mr. Wang ya ce, har kullum Sin da Rasha na sa kaimi ga cimma matsaya daya cikin shawarwarin bisa babban tsari na kiyaye zaman lafiyar yankin gabas ta tsakiya da hana yaduwar makaman nukiliya. Ban da haka kuma, Sin za ta hada kai da Rasha don sa kaimi ga bangarorin daban-daban dake da nasaba da wannan batu su yanke shawara a siyasance a samu kai wa ga matsaya daya cikin adalci a wannan muhimmin lokaci na shawarwarin.

A nasa bangare, Sergei Lavrov ya nuna cewa, Rasha na fatan kara hadin gwiwa da kasar Sin cikin shawarwarin don sa kaimi ga cimma nasara .

Haka kuma, a wannan rana Mr Wang ya gana da takwaransa na kasar Amurka John Forbes Kerry. A lokacin ganawar Mr Wang ya ce, yanzu bangarorin daban-daban na kusan kai wa ga matsaya daya kan batun nukiliyar Iran, don haka yana fatan za'a nace ga bin ka'idar adalci a mataki-mataki, kana da warware wasu batutuwa da babu tabbaci tare da kai ga cimma matsaya daya.

John Forbes Kerry kuma ya ce, Amurka na fatan kara hadin gwiwa da kasar Sin don a kokarta wajen cimma matsaya daya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China