Rigakafi da sanya ido kan annobar cututtuka masu yaduwa sun kasance muhimman kalubale ga gamayyar kasa da kasa, in ji shugaba Xi Jinping, tare da yin kiran da a karfafa huldar dangantakar kasa da kasa wajen sanya ido.
Kyautata ayyukan kiwon lafiyar jama'a da tabbatar da kishin lafiyar al'umma na kasancewa wani muhimmin aiki da gwamnatin kasar Sin ke maida hankali a kai sosai ganin muhimmancinsa.
Shugaban kasar Sin ya bayyana cewa kasarsa za ta ci gaba da huldar dangantaka tare da kungiyar Bill da Melinda a wannan fanni.
Kasar Sin tana ba da muhimmanci sosai wajen rage talauci kuma a wannan fannin ta samu ci gaba sosai. Kuma za ta kara himmatuwa ta yadda za ta kai ga cimma burinta na gina wata al'umma mai cike da wadata yadda ya kamata nan da shekarar 2020.
Shugaban kasar Sin ya kuma bayyana cewa kasar Sin za ta dauki nata nauyi a cikin tsarin bunkasuwa na MDD na bayan shekarar 2015 kuma a shirye take ta yi aiki tare da gamayyar kasa da kasa domin rage kaifin talauci a duniya.
A nasa bangare mista Bill Gates, shugaba na biyu na kungiyar Bill da Melinda, ya bayyana cewa kasar Sin ta taimaka, ta hanyoyi daban daban, ga kokarin hadin gwiwa na gamayyar kasa da kasa domin yaki da annobar cutar Ebola, kuma ta yi muhimmin aikin da aka nuna yabo domin ya sanya ido kan cutar kanjamau. A cewarsa, kasar Sin ta nuna babban misali ga duniya ta hanyar taka muhimmiyar rawa na shugabanci wajen rage talauci.
Tare da kuma bayyana burinsa da fatansa na kara karfafa dangantaka tare da kasar Sin a fannin kiwon lafiyar jama'a. (Maman Ada)