A cikin sakon nasa, Xi Jinping ya bayyana cewa, bana shekara ce cika shekaru 10 da kafa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen Sin da Najeriya, kuma kara bunkasa huldar dake tsakanin kasashen biyu ya dace da babbar moriyar kasashen biyu da jama'arsu. Ya ce, Sin na mai da hankali sosai wajen bunkasa huldar dake tsakanin kasashen Sin da Najeriya, tana kuma fatan samun hadin kan bangaren Najeriya domin daga huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashenta da Najeriya zuwa wani sabon mataki. (Sanusi Chen)