Wang ya bayyana cewa, makasudin yin wannan muhawarar a yau shi ne, na farko, koyon darasi daga tarihi, da nanata alkawarin da aka yi kan kundin tsarin mulkin MDD, na biyu, kokarin samar da makoma mai kyau, da neman samun wata sabuwar hanya a fannin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya a cikin sabon yanayi.
A wannan rana, ban da jagorantar muhawarar kwamitin sulhu, Wang Yi ya kuma gana da takwarorinsa na Malaysia Anifah Aman, da na Rasha Sergei Lavrov, da babban sakataren MDD Ban Ki-moon, da shugaban babban taron MDD Sam Kahamba Kutesa da sauransu. Abu mafi muhimmanci shi ne, ya isar da wani muhimmin sako a fili, wato Sin tana kokarin tabbatar da tsarin duniya mai kwanciyar hankali, tare da kokarin kiyaye shi, a maimakon kawo masa kalubale.(Fatima)