in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Samun nasara tare ita ce hanya mafi dacewa wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen duniya
2015-02-03 14:56:04 cri

A jiya ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwarorin aikinsa na kasashen Rasha Sergei Lavrov da kuma ta kasar Indiya Swaraj karo na 13 a nan birnin Beijing, inda Wang Yi ya bayyana cewa, ya kamata a yi watsi da tsohuwar hanyar wani ya cimma nasara wani kuma akasin haka a yayin raya dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, neman sabuwar hanyar samun nasara tare ita ce hanya mafi dacewa a wannan fanni.

Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta gabatar da kafa sabuwar dangantaka a tsakanin kasashen duniya ne bisa tushen yin hadin gwiwa da samun nasara tare, wanda shi ne manufofin harkokin wajen kasar Sin na samun adalci da bude kofa da kuma samun moriyar juna, kana hakan ya bude sabuwar hanya ga kasa da kasa wajen daidaita dangantakar dake tsakaninsu.

Wang Yi ya kara da cewa, bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya, da bunkasuwar sadarwa a tsakanin al'ummar duniya, sun taimaka wajen saukaka yin mu'amala a tsakanin kasa da kasa a duniya. Don haka, samun nasara tare cikin hadin gwiwa ya dace da halin da duniya ke ciki a halin yanzu wanda ya dace da sabuwar bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen duniya.

Ban da wannan kuma, Wang Yi ya ce, yin hadin gwiwa da samun nasara tare sun dace da burin kasashe maso tasowa. Sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin kasa da kasa bisa tsarin demokuradiyya da cin gajiyar 'yancin tsarin kasa da kasa a tsakanin kasashen duniya su ne abin da kasashe masu tasowa ke bukata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China