in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Amurka sun zanta ta wayar tarho
2015-02-11 15:13:47 cri

A Larabar nan ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin, da takwaransa na Amurka Barack Obama, suka zanta ta wayar tarho, inda suka taya juna murnar shiga sabuwar shekara, tare da cimma matsaya guda a fannin karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, a wani mataki na neman samun ci gaba ciki dogon lokaci, ta yadda za a samu karin bunkasuwa ta fuskar raya dangantakar sassan biyu.

Ana dai sa ran shugaba Xi Jinping zai halarci bikin tunawa da cika shekaru 70 da kafuwar MDD a watan Satumbar bana, bisa kuma wannan ne Shugaba Obama ya gayyace shi Amurka domin gudanar da ziyarar aiki. Tuni kuma shugaban na Sin ya amince da wannan gayyata, ya yin da kuma kasashen biyu suka amince da share fagen tabbatar da nasarar wannan ziyara. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China