Ministan ya jaddada matsayin gwamnatin kasar Sin ne game da abin da ke faruwa a yankin Hong Kong lokacin da ya gana da Shugabannin kasar Amurka a fadar White house da kuma ma'aikatar harkokin kasar inda yace wannan ka'ida ce da ta shafi huldar da ke tsakanin kasa da kasa.
Boren mai taken mallakan tsakiyar an fara shi ne a safiyar ranar lahadin data gabata a cibiyar gwamnatin yankin dake Admiralty a cikin garin na Hongkong daga baya kuma aka samu karuwan masu zanga zanga a tsakiyar birnin da unguwannin causeway bay da Mongkok abin da ya kawo cunkoson ababen hawa da rufe makarantu.
A game da hakan Mr.Wang yace yana da imanin cewa kowane kasa kowane al'umma ba wanda zai amince da wannan ayyukan rashin da'a wanda ya lalata zaman rayuwar al'umma.