A jiya Laraba 1 ga wata ne shugaban kasar Amurka Barack Obama ya gana da ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi a fadarsa ta white house
Yayin ganawar, Mr. Obama ya darajanta gudunmawar da Sin take bayarwa kan harkokin duniya, kuma ya sa ran alheri ga ziyarar da zai kawo a watan Nuwamba mai zuwa, inda zai zurfafa mu'ammla da shugaba Xi Jinping kan yadda za su kafa sabuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu, da ciyar da hadin gwiwa tsakaninsu gaba daga dukkan fannoni, da tinkarar wasu batutuwa da kalubaloli na kasa da kasa da na shiyya-shiyya tare, ciki hadda batun sauyin yanayi, cutar Ebola, ta'addanci da sauransu.
A nasa bangare, Mr. Wang ya ce, Sin na maraba da ziyarar da shugaba Obama zai kawo kasar Sin , kuma yana fatan kara hadin gwiwa da kasar ta Amurka ta fuskar zurfafa amincewa da juna, da habaka hadin kai a dukkan fannoni, da kuma sa kaimi ga kafa sabuwar dangantaka tsakaninsu yadda ya kamata.
Kazalika, a wannan rana Mr. Wang ya gana da takwaransa na kasar Amurka John Kerry da sakataren tsaron kasar Amurka Charles Timothy Chuck Hagel, inda suka yi musanyar ra'ayi kan wasu batutuwa dake jawo hankalin kasashen biyu sosai tare da kai ga cimma matsaya daya. (Amina)