in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na nacewa ga kiyaye zaman lafiya da karko a yankinta, in ji ministan harkokin waje na kasar Sin
2014-04-14 20:52:29 cri
Bayan kammala tattaunawa tsakanin ministocin harkokin waje kasashen Sin da Jamus karo na hudu, Jami'an jami'an kasashen biyu sun yi gana da manema labaru a ran litinin din nan 14 ga wata.

A lokacin ganawar, Mr Wang Yi, ministan harkokin waje na kasar Sin ya yi baynin bayani a kan halin da Sin ke ciki a kewayentayankin dake kewayen kasar Sin ke ciki. Yana mai cewa da farko, Sin na da dangantakar mai kyau da kasashe dake makwabtaka da ita, kuma ana kara zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu, sannan bunkasuwar da Sin ta samu ta samar da babban zarafi ga wadannan kasashe.

Na biyu kuwa inji shi wadansu bambancin ra'ayi da aka dade ana fuskanta nsun sake kunno kai a wadannan lokutan da suka gabatakwanakin baya ne saboda wasu kasashe sun sabawa yarjejeniyar da suka daddale da kasar Sin a baya, kuma sun tada zaune tsaye.

A na uku kuma,yace kasashe a wannan yanki har ma da al'ummar duniya, kamata ya yi, su kyautata matsayinsu kan halin da ake ciki yanzu bisa daidaici da adalci a dukkan fannoni.

A na hudu, Ministan yace Sin za ta ci gaba da daukar manufofin diplomasiyya kan na kokarin sada zumunta da kasashe dake makwabtaka da ita dake kokarin sada zumunci, da yin hadin gwiwa da da su don kawo moriyar juna.

Mr Wang ya ce ba ma kawai Sin ta zama mataki mai inganci wajen ba da gudunwama ga bunkasuwar wannan yanki ba, har ma ta kasance mai kiyaye zaman lafiya da karko a yankin, don haka yace kasar na da imanin cewa, za ta hada kai da sauran kasashe nan gaba domin ba da gudunmawa wajen samar da makoma mai haske ga gabashin Asiya da ma dukkan fadin nahiyar Asiya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China