in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya jaddada bukatar samar da ci gaba cikin lumana game da batun Taiwan
2015-03-05 11:02:23 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada bukatar samar da ci gaba cikin lumana game da batun Taiwan.

Shugaban ya yi wannan kalami ne lokacin da ya shiga cikin tattaunawar dake wakana da 'yan majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa na CPPCC wadanda ke taronsu na shekara a nan birnin Beijing.

Shugaban ya bukaci a nuna kishin kasa a kowane lokaci tare da yin taka tsantsan na kare ci gaba cikin lumana daga dukkan bangarori.

Ya ce, masu neman 'yancin Taiwan da ayyukansu na barazana ga hadin kan kasa da dunkulewar yankin gaba daya. Yana mai bayanin cewa, suna son tada hankalin 'yan hamayya da kungiyoyi a duk fadin kasar domin lalata tunanin da ya kai ga dinkewar da iyayen kasa suka yi.

Shugaba Xi har ila yau ya bayyana cewa, babban cikas ga ci gaban zaman lafiya a tsakanin bangarori da dama babban barazana ne ga zaman lafiya da ci gaba, don haka ya ce, kada a amince da hakan ko kadan.

Babban abin da ke gaban komai shi ne ci gaban babban yankin kasar ta Sin, in ji shugaba Xi. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China