in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya jaddada tabbatar da ganin jama'a sun ci gajiyar gyare-gyaren da ake a kasar
2015-02-27 20:22:35 cri

A yau da safe ne, shugaban kasar Sin ya shugabanci taro karo na 10 na kungiyar da ke jagorantar ayyukan zurfafa gyare-gyaren da kasar Sin take yi a gida a dukkan fannoni.

A jawabinsa yayin taron, shugaba Xi ya jaddada cewa, ya zama dole a daidaita ayyukan yin gyare-gyare a gida ta hanyar kimiyya, tare da mai da hankali kan gudanar da matakan yin gyare-gyaren da aka tabbatar a wasu muhimman taruka. Sa'an nan kamata ya yi a yi gyare-gyare a gida bisa dokoki, kana a kyautata dokoki yayin da ake yin gyare-gyare a gida. Wajibi ne a fito da wasu nagartattun matakan a-zo-a-gani, wadanda za su samu amincewa daga fararen hula. Dole ne kuma a kawar da duk wani abin da zai kawo cikas yayin da ake aiwatar da gyare-gyare a kasar, kana kuma tilas ne a sauke nauyi yadda ya kamata, a kokarin ganin an fahimci kyakkyawan amfanin ayyukan yin gyare-gyaren, ta yadda fararen hula za su kara cin gajiyar aikin yin gyare-gyaren da ake a kasar. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China