in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashe 6 game da batun nukiliya na Iran
2015-03-30 10:31:12 cri
A Jiya Lahadi a birnin Lausanne da ke kasar Swiss, ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashe 6 game da batun nukiliya na kasar Iran, don tattauna muhimman matsalolin da ake fuskanta cikin shawarwari.

Mista Wang ya ce, yanzu, an shiga wani muhimmin mataki cikin shawarwarin, ya kamata bangarorin daban daban su taka muhimmiyar rawa, don ba da gudummawa ga shawarwarin. Matsalolin da ake fuskanta na da alaka tsakaninsu, ya kamata ko wane bangare ya yi sassauci da kuma tsaida kudurin siyasa don warware su tun da wuri.

A nasu bangare kuma, sauran ministocin sun bayyana cewa, yanzu, ana fuskantar babbar dama cikin shawarwarin, kuma wannan ya danganta da kokari daga bangarorin daban daban. Ya kamata bangarorin su kiyaye wannan sakamakon da aka samu, don cimma daidaito, da warware matsalolin dake fuskanta, ta hakan za a samu cigaban shawarwarin.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China