in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya bayyana ra'ayinsa kan bunkasuwar hadin gwiwar Sin da Afirka
2015-01-17 20:19:13 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana ra'ayinsa dangane da matakan da suka dace a dauka, domin ciyar da hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka gaba.

Wang ya bayyana wasu matakai uku yayin da yake jawabi a birnin Kinshasan kasar Congo a jiya Jumma'a a gabanin kammala ziyarar aikin da ya gudanar a kasashe biyar na nahiyar ta Afirka.

Mr. Wang ya ce, ziyarar tasa ta wannan karo na kunshe da sakamako 3. Abu na farko shi ne batun hadin gwiwa, ta yadda burin kasar Sin da na kasashen Afirka game da neman bunkasuwa ya yi kama da juna, don haka ya dace a gudanar da hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu, domin samun ci gaba tare.

Na biyu ya ce, kamata ya yi a gudanar da neman bunkasuwar Sin da Afirka cikin hadin gwiwa, bisa zumuncinsu na gargajiya, da kuma ciyar da bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka gaba, sakamakon manyan albarkatun sassan na dan Adam da na halittu da nahiyar take da su, ta yadda za a iya ba da tallafi ga dukkanin jama'ar Sin da Afirka, har ma da sauran jama'ar kasashen duniya.

Na uku kuwa shi ne batun neman kyautatuwa. Inda a yayin da sabuwar hanya, da sabon ra'ayin hadin gwiwar Sin da Afirka ke bada babbar dama ga inganta hadin gwiwar bangarorin biyu, a hannu guda ana sa ran samun kyautatuwar musayar cinikayya, da hanyoyin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, bisa kokarin bangarori biyu.

Wang Yi ya kara da cewa, ra'ayoyin kasar Sin kan bunkasa hadin gwiwar Sin da Afirka, sun samu amincewar kasashen Afirka, matakin da zai kara bunkasa hadin gwiwarsu a fannin cimma moriyar juna, tare da inganta sabuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China