Yayin ganawar tasu, jami'an sun jaddada yanayin zumunta, da hadin gwiwa dake tsakanin Sin da kasashen Afirka. Sun kuma yi musayar ra'ayoyi game da batun yiwa kwamitin sulhun MDD kwaskwarima, da batun kara hadin gwiwar dake tsakaninsu.
A nasa bangare Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin na goyon bayan manufar yiwa kwamitin sulhun MDD kwaskwarima, da kara yawan wakilci daga kasashe masu tasowa musamman daga kasashen Afirka a kwamitin na sulhu, da ma samar da karin ikon fadar albarkacin baki na sauran kasashe.
Ya ce kamata ya yi a aiwatar da kwaskwarimar ta hanyar tattaunawa bisa tsari na dimokuraddiya, da cimma daidaito, da kuma neman hanyoyin warware matsaloli.
A daya bangaren, bangaren kasashen Afirka ya bayyana cewa, zai ci gaba da tsaiwa tsayin daka kan matsayin kungiyar hadin kan Afirka ta AU. (Zainab)