Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amince gayyatar da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi masa yayin da suka buga wayar tarho da juna a ranar 11 ga wata, kuma ya tabbatar da kai ziyara a kasar Amurka tare da halartar bikin cika shekaru 70 da kafa MDD a watan Satumba na bana. Wannan ne karo na farko da Xi Jinping zai kai ziyara a kasar Amurka bayan da ya hau kujerar shugaban kasar Sin, don haka ziyarar ta jawo hankalin kasa da kasa sosai.
Mataimakin shugaban kwalejin nazarin batutuwan kasa da kasa na kasar Sin Ruan Zongze ya bayyana cewa, shekarar badi shekara ce da za a yi zaben shugaban kasar Amurka. Wannan ganawa tsakanin shugabannin Sin da Amurka za ta sa kaimi ga bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata har ma da kiyaye ta zuwa sabuwar gwamnatin kasar Amurka.
Shugaban sashen Amurka na kwalejin nazarin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa na kasar Sin Da Wei ya bayyana cewa, wannan ziyara za ta taimakawa kasashen biyu wajen daidaita matsalolinsu, kamar batun teku na kudu na Sin, batun tsaron internet da sauransu, da magance samun rikici a kan dangantakarsu, da kawar da cikas yayin da ake raya dangantakar dake tsakaninsu.
A wannan rana kuma, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Amurka Anthony Blinken dake ziyara a nan birnin Beijing ya tattauna tare da bangaren Sin kan shirye shiryen ziyarar shugaba Xi Jinping a kasar Amurka. (Zainab)