Takaitaccen bayani kan kasar Saudiyya Saudiyya tana kudu maso yammacin nahiyar Asiya a zirin Larabawa, a gabas ta yi makwabtaka da yankin Gulf, kuma a yamma ta yi makwabtaka da tekun Bahar Maliya, ta yi iyaka da kasashen Jordan da Iraqi da Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa da Oman da Yemen da dai sauransu |
Takaitaccen bayani kan kasar Mali Babban birnin kasar Mali shi ne Bamako, shugaban kasar Mali shi ne Amadou Toumany Toure, a watan Mayu na shekarar 2002 ya ci zaben zama shugaban kasar, kuma a watan Mayu na shekarar 2007, ya sake cin zaben zama shugaban kasar, a watan Yuni na shekarar ya yi rantsuwar kama aiki |
Takaitaccen bayani kan kasar Senegal Kasar Senegal tana yammacin Afirka. Ta yi iyaka da kasar Mauritania wadda kogin Senegal ya raba su, tana dab da kasar Mali ta gabas, da kasashen Guinea da Guinea-Bissau ta kudu, kuma tana bakin tekun Atlantic. Fadin kasar ya kai muraba'in kilomita dubu 196.7 |
Takaitaccen bayani kan kasar Tanzania Hadaddiyar Jamhuriyar Tanzania na kunshi da yankuna 2, wato su babban yankin Tanganyika da tsibirin Zanzibar. Fadin kasar ya kai murabba'in kilomita dubu 945 da wani abu, ciki ya hada da fadin tsibirin Zanzibar na kilomita 2657. |
Bayani game da kasar Mauritius Fadin kasar Mauritius ya kai muraba'in kilomita dubu 2 da arba'in. Ita wata kasa ce dake kan tsibirai da yawa a kudu maso yammacin tekun Indiya. Muhimmin tsibiri na kasar Mauritius mai tazara kilomita dari 8 daga gabashin kasar Madagascar. Sauran tsibirai sun hada da tsibirin Rodrigues da Agalega da Cargados Carajos. Kuma tsawon gabar teku na kasar ya kai kilomita 217. |
|